Kasashen Musulmi Da Dama Sun Fara Azumin Watan Ramadan

A jiya Talata da marece ne dai kasashe da dama na musulmi su ka sanar da ganin jaririn wata Ramdana mai alfarma da hakan ya

A jiya Talata da marece ne dai kasashe da dama na musulmi su ka sanar da ganin jaririn wata Ramdana mai alfarma da hakan ya mayar da wannan rana ta 18 ga watan Febrairu a matsayin daya ga watan Azumi.

Daga cikin wadannan kasashen da aka fara azumi a yau da kawai Saudiyya, Lebanon, Qatar, UAE, Kuwait da kuma kasar Sudan.

A Falasdinu,babban mufitin birnin Kudus, ya sanar da cewa ganin watan Azumi a jiya da marece, saboda haka yau ne ranar Farko ta watan na azumi.

 A kasar Afghanistan,Djibouti, da Somaliya suna cikin kasashen da su ka sanar da fara azumi a yau Laraba.

 Da akwai wasu kasashen da su ka sanar da cewa, sai gobe Alhamis ne za a fara azumin watan na Ramadana, da su ka hada Masar, Jordan, Syria, Indonesia da Malyasia.

 Su kuwa kasashen Iran, India, Pakitsan, BAngaladesh, Oman da Tukiya sun sanar da jiya Talata a matsayin cikon watan Sha’aban.

A kasar Moroko da Murtaniya an sanar da cewa, yau Laraba za a ci gaba da duban watan Ramadan, bayan da a jiya ba a jiya ganinsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted