Search
Close this search box.

Kasashen Mali,Nijar Da Burkina Faso Sun Kafa Kungiyar  Hadakar  Kawancen Kasashen Yankin Sahel Uku

Kasashen uku wadanda su ka yi taro a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, sun rattaba hannu akan yarjejeniyar kafa kungiyar “Hadakar Kawancen Kasashen Yankin Sahel”

Kasashen uku wadanda su ka yi taro a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, sun rattaba hannu akan yarjejeniyar kafa kungiyar “Hadakar Kawancen Kasashen Yankin Sahel” a jiya Asabar.

Bayan wannan taron an fitar da bayani wanda ya ce; mahalarta taron sun hada shugabannin soja na kasashen, Nijar janar Abdurrahman Tiani, Mali Ibrahim Traoré da kuma Asmi Guwaita Burkina Faso.

Har ila yau, bayanin ya ce; Kasar Mali ce za ta jagorantar wannan sabuwar kungiyar na shekara daya. Ita kuwa Burkina Faso za ta karbi bakuncin taron ministocin kasashe.

Har ila yau,mahalarta taron sun cimma matsaya akan kafa Bankin zuba HJannun jari a tsakaninsu, kamar kuma yadda su ka jaddada wajabcin aiki tare a tsakaninsu a fagagen diplomasiyya da yin Magana da harshe daya.

Wasu fagagen aiki tare a tsakanin kasashen sun kunshi aikin gona, da samar da abinci, ruwa, muhalli, makamashi da kuma ma’adanai.

A karkashin yarjejeniyar da kasashen uku su ka rattaba hannu akai, wanda ya shafi tsaro, kai wa kowace daya daga cikin kasashen hari, daidai yake da kai wa dukkanin yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments