Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya tare da takwaransa na Saudiyya
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Saudiyya, Faisal bin Farhan a yammacin ranar Laraba.
Araqchi, wanda a lokacin yana gudanar da ziyarar aiki a birnin Beijing na kasar China domin tattaunawa da jami’an kasar, ya yi magana da takwaransa na Saudiyya, Faisal bin Farhan.
A yayin kiran, bangarorin biyu sun tattauna sabbin abubuwan da suka faru a yankin, inda suka jaddada bukatar ci gaba da kokarin diflomasiyya da hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin hana karuwar tashe-tashen hankula.