Kasashen Ghana Da Burkina Faso Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyoyi 7

Ghana da Burkina Faso sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi na hadin gwiwa don samar da tsaro a kan wasu muhimamman hanyoyi da ƴan kasuwa

Ghana da Burkina Faso sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi na hadin gwiwa don samar da tsaro a kan wasu muhimamman hanyoyi da ƴan kasuwa ke amfani dasu don hada-hadar kayayyaki a yankin sahel.

Cikin yarjeniyoyi 7 da wakilan kasashen 2 suka sanyawa hannu akai, sun hada da samar da sabon tsarin tsaro  da dakile ayyukan ta’addanci a yankunan , sai kuma shawo kan matsalar ambaliyar ruwa daga kogin Bagre wanda aka dade ana fuskanta a arewacin Ghana.

Bugu da kari, kasashen 2 sun amince da fitar da sabon tsarin hadin kai a iyakoki wanda zai kara kulla kayakkyawar alaka tsakanin garuruwan dake iyakar da warware matsalolin da ake fuskanta.

Haka zalika kasashen sun tattauna hanyoyin samar da ci gaba da kara kulla alakar kasuwanci mai karfi kuma mai dorewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted