Kasashen Afirka: Ba  Domin Sadaukar Da Kanmu Ba Da Faransa Ba Ta Sami ‘Yanci Daga ‘Yan Nazi Na Jamus Ba

Kasashen Tchadi da Senegal sun yi wa Faransa tuni akan cewa ba domin sadaukar da kan da kasashen na Afirka su ka yi ba ,

Kasashen Tchadi da Senegal sun yi wa Faransa tuni akan cewa ba domin sadaukar da kan da kasashen na Afirka su ka yi ba , to da Faransa ba ta sami ‘yanci daga mamayar da ‘yan Nazi su ka yi ma ta ba.

Kasashen biyu na Afirka sun yi tir da furucin shugaban Faransa Emmanuel  Macron da ya ce, kasashen Afirkan sun ki  yi wa kasarsa godiya duk da cewa ta taimake su a fada da ta’addanci.

Macron ya ce, shiga cikin yaki da kasar tasa ta yi wajen fada da ta’addanci a yankin Sahel tun 2013, daidai ne, amma kuma shugabannin nahiyar ta Afirka sun mance da wannan taimakon da Faransan ta yi musu, kuma ko godiya ba su yi ma ta ba.

Shugaban kasar ta Faransa dai ya bayyana hakan ne a yayin ganawar shekara-shekara da yake yi da jakadun kasarsa, inda ya kara da cewa, ba domin wancan tsoma bakin da Faransan ta yi ba, to da wadannan shugabannin na yanzu ba su sami damar da za su yi mulkin kasashensu masu ‘yanci ba.

Shugaban kasar na Faransa ya yi Magana cikin isgili yana mai cewa: “Wannan ba shi da muhimmanci, lokacin da za su yi godiya zai zo.”

Bugu da kari,shugaban na kasar Faransa ya ce ya kuma ce, janye sojojinmu da mu ka yi daga kasashen Afirka, ya kasance ne ta hanyar yin shawar da wadannan kasashen, illa iyaka mun ba su damar su fara sanar da yin hakan, saboda mu mutane ne masu ladabi.!

Da alama shugaban kasar ta Faransa yana yin ishara ne da kasashen Senegal da Chadi da su ne na bayan nan da Faransan ta janye sojojinta daga cikinsu.

 Sai dai Tchadi ta yi watsi da furucin na shugaba Macron tare da cewa ya kamata Faransa ta koyi girmama mutanen Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments