Atisayen sojin Iran na “Manzon Allah Mai Girma na 19” yana ci gaba da gudana da jan hankali a matsayin matakin shirin mayar da martini mai girma kan duk wata barazanar makiya
An fara kaddamar da atisayen soji mai girma a kasar Iran ne mai taken “Manzon Allah Mai Girma Karo na 19 da ya hada sojojin Iran da na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar da ya samu halartar bangarori daban-daban da rundunar kasar na musamman da nufin kara shiri da kuma hadin kai wajen tunkarar duk wani matakin wuce gona da iri da kasar ta Iran zata iya fuskanta daga makiya.
An fara atisayen mataki na farko na hadin gwiwar tsaron sararin samaniya a kewayen cibiyar makamashin Nukiliyar Iran da ke cibiyar Natanz, a daidai lokacin da sassan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na sama suka gudanar da cikakken tsaro ga cibiyar.