Jagoran Juyin Juyala Halin Musulunci a nan Iran Imam Aya. Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da firay ministan kasar Iraki Muhammad Shia Al-Sudani wanda ya kawo ziyarar kwana guda a nan birnin Tehran a jiya Laraba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa Al-sudani ya shigo kasar Iran ne a safiyar jiya Laraba don tattaunawa da shugaban kasar Iran masoud Paezeshkiyan kan al-amura da dama, banda haka ya maida martani ne ga ziyara irinsa wanda shugaban Pezeshkiyan ya kai kasar ta Iraki inda ya ziyarci Bagdza, Najaf , Karbala da kuma yankin kurdawa na kasar Iraki.
A gaban jagora kuma Al-sudani ya bayyana cewa gwamnatinsa tana kula da ‘rundunar Hashdusha bi’ don kare kasar daga duk wata barazanan da zata bullo mata nan gaba. Kuma sun ne zasu kare kasar daga duk wata barazana ta ayyukan ta’addanci, ya kuma bayyana cewa manufar kasar Irakice taimakawa al-ummar Falasdnu a Gaza.