Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa a cikin shekarun da suka gabata gwamnatin kasar Amurka yana kurakurai masu yawa dangane da kasar Iran.
Jagoran ya kara da cewa yana Magana ne da wadanda suke tsoron abinda yan siyasar kasar Amurka suke fada.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Laraba 8 ga watan daya na shekara ta 2025, a lokacinda yake ganawa da mutanen Qum wadanda suka zo wajensa don tunawa da yunkurin shekara 1356 H.SH.
Jagoran ya kara da cewa bayan kura-kuran da suka yi a baya har yanzun suna maimaita wadannan kura kuran.
Jagoran ya kara da cewa a halin yanzu aikin gidajen radiyo da talabijin na kasa, da kuma hukumar watsa shirye-shiryen addini ne su yaye labule wa mutane kan cewa farfagandar da makiya suke yi dangane da kasar Iran karya ce. Su bayyana su kowa ya sani. Kamar dai yadda mutanen Qum sukayi a shekara ta 1356.
Daga karshen jagoran ya bayyana cewa gaskiya ne, iran tana huldar jakadanci da kasashen turai amma take wani abu ya hadata da Amurka. Yace: haka ya faru ne saboda Amurka ta yi arata babba a kasar iran bayan nasarar juyin juya halain musulunci a shekara 1979, don haka tafi sauran kasshen kiyayya da kuma kuntatawa kasar Iran don haka idan mun dawo da ita kusa zamu kara cutuwa ne.