Kasar Iran Ta Saki ‘Yar Kasar Italiya Da Ta Kama Kan Keta Dokokin Kasarta

Kasar Iran ta saki ‘yar jaridar Italiya da ake tsare da ita saboda keta wasu dokokin kasar ta Iran Ofishin fira ministan kasar Italiya ya

Kasar Iran ta saki ‘yar jaridar Italiya da ake tsare da ita saboda keta wasu dokokin kasar ta Iran

Ofishin fira ministan kasar Italiya ya sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Mahukuntan Iran sun Cecilia Sala ‘yar jarida ‘yar kasar Italiyan nan da ake tsare da ita a Iran bisa zargin keta dokokin kasar, inda ta tabbatar da cewa: Sala tana kan hanyarta ta komawa Italiya.

Sanarwar ta ce: Mahukuntan Iran sun saki Madam Sala daga gidan yari ne bayan tattaunawa mai tsanani ta diflomasiyya, kuma jirgin da yake dauke da ita ya bar birnin Tehran ya nufi Italiya.

A cikin wani sakon twitter a shafin dandalin “X”, Fira Ministan Italiya Giorgia Meloni ya rubuta cewa: “Jirgin da ya dauko Cecilia Sala daga birnin Tehran domin dawo da ita gida mahaifarta ya tashi kuma yanzu haka yana kan hanyarsa ta zuwa Italiya.

An kama Madam Cecilia Sala ce a ranar 19 ga watan Disamban shekara ta 2024 da ta gabata, bisa zargin keta dokokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments