Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce: Amurka na kokarin rama gazawarta a Iran
A martanin da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya mayarwa masu tambaya kan dalilin da ya sa Iran ke tattaunawa da kasashen Turai kuma tana da alaka da su, yayin da ba ta son gudanar da zaman tattaunawa da Amurka, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya jaddada cewa: Amurka ta mallaki Iran, amma an kore ta daga cikinta. Don haka ba za ta yi watsi da ita cikin sauki ba, yana mai nuni da cewa Amurka ta gaza a Iran, kuma tana neman daukan fansa kan dalilan wannan gazawarta.
A yayin ganawarsa da dubban al’ummar birnin Qum a yau Laraba, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar juyin juya halin Musulunci na ranar 19 (wanda ya zo daidai da ranar 9 ga watan Decemban sheakara ta 1978), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya yi nuni da cewa: A wancan lokacin Iran tana karkashin mulkin zamanin Sarakunan Pahlavi da ta kasance katanga ce da take kare manufofi da masalahar Amurka kuma daga tsakiyar wannan katanga ce wannan juyin juya hali ya kunno kai saboda kura-kuran Amurkan ta aikata lamarin da ya rusa lisafinta tare da korarta da yin watsi da ita.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Amurkawa sun tafka kurakurai da dama a lissafin da suka yi kan kasar Iran tsawon shekaru da dama.