Shugaban kasar Iran a wani jawabin hadin giwa da firay ministan kasar Iraki wanda ya kawo ziyara kasar Iran na kwana guda a jiya Laraba a nan Tehran, sun jaddada bukatar aiki tare da a yaki da ayyukan ta’adanci a kasar da kuma da kuma karfafa dangantakar tattalin arzikin kasashen biyu daga ciki har da aikin layin dogo daga Chalamce da kuma birnin Basra.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ya nakalto shugaba Pazeshkiyan yana cewa batun tsaron kasashen biyu da kuma al-amuran tattalin arziki musamman aikin layin dogo tsakanin Basra da chalamce.
Shuwagabannin biyu sun tattauna abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya da kuma yadda zasu shafi kasashen yankin.
Shugaba Pezeshkiyan ya godewa mutane da gwamnatin kasar Iraki kan ziyarorin da miliyoyin kasar Iran suka a wurare daban daban a kasar a farkon shekarar da ta gabata.
Har’ila yau Firay ministan na kasar Iraki ya ziyarci shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bakir Qalibof. Inda suka tattauna al-amura da dama daga ciki har da batun tsaro a yankin Asiya ta kudu musamman dangane da halin da ake ciki a gaza da kuma kasar Siriya.