A wani babban kalubale, zababben shugaban Amurka Trump ya sake yin barazana ga Gaza da wani sabon salo
A karo na biyu a cikin ‘yan kwanakin nan, zababben shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar mayar da yankin Zirin Gaza Jahannama a ga Falasdinawa, a wani yanayin barazanarsa mai cike da hadari na ci gaba da nuna makauniyar goyon bayansa ga gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yar mamaya da kuma rashin la’akari da wahalar da dan Adam ke fuskantaa yankin.
Falasdinawa a Gaza sun tabbatar da tsayin daka na tarihi wajen tunkarar ‘yan mamaya, yayin da ake ci gaba da gwagwarmaya daga waannan al’ummar zuwa al’ummar da ke biye mata, don samar da abin koyi na azama da dagewa kan maido da hakki da ‘yantar da kasarsu da aka mamaye da karfi.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sabunta amincinsa ga gwamnatin ‘yan mamaya a lokacin da yake magana a baya-bayan nan inda ya ce: “Shi ne babban abokin yahudawan sahayoniyya har abada.”
Bayanan da manazarta suka bayyana a matsayin wauta karara, tare da bayyana cewa shugabannin Amurka suna nuna makauniyar soyayya da goyon baya maras iyaka ga laifuffukan ‘yan mamaya.