Wani dan majalisar dokokin kasar Burtaniya mai suna John Macdonal ya bukaci majalisar dokokin kasar Burtaniya ta kori jakadiyar HKI daga birnin London ta kuma dorawa HKI takunkuman tattalin arziki masu muni, saboda kissan kare dangin da take yi a Gaza, kimani watani 15 da suka gabata.
Dan majalisar ya bayyana cewa a halin yanzu yara kanana a zirin gaza, suna mutuwa saboda yunwa da sanyi da yunwa saboda kofar ragon da HKI ta yiwa yankin. Ruwa da abinci da magunguna duk basa shiga yankin.
Macdon ya kara da cewa dukkan kasashen duniya sun tabbatar da cewa abinda HKI take yi a gaza, kissan kiyashi ne, wanda babu wanda ya isa ya musanta haka, saboda abune wanda yake a fili ga kowa. Laifukan yakin da HKI take aikatawa a Gaza a fili suke, ba’a bukatar wani bincike.
John Macdon dai dan majalisar dokokin kasar Burtaniya ne mai zaman kansa, ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar Burtaniya da majalisar dokokin kasar su dauki matakan da suka dace kan HKI.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne dai, jiragen yakin HKI suka fara ruwan boma-bomai a kan mutanen gaza, kuma shuwagabannin yahudawan sun tabbatar da cewa manufarsu ita ce shafe al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan da ginawa yahudawan sahyoniya matsugunai a wurin