Mutane 11 Ne Aka Kashe Sannan Aka Kona Gidaje 31 A Rikicin Kabilanci A Jihar Jigawa

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu sannan aka kona gidaje har 31 sanadiyyar rikicin kabilanci a garuruwan Jahun da Gululuha na karamar hukumar Miga

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu sannan aka kona gidaje har 31 sanadiyyar rikicin kabilanci a garuruwan Jahun da Gululuha na karamar hukumar Miga a jihar Jigawa na tarayyar Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta najeriya ta bayyana cewa al-amarin ya faru ne a ranar Jumma’an da ta gabata, kuma Sulaiman Abubakar Jahun daya daga cikin wadanda aka kashe tsayansa a cikin rikicin ya fada mata cewa a rannan yana cikin gidansa sai aka zo masa da labarin cewa ana fada tsakanin Hausawa da Fulani. Ya ce a lokacinda ya isa wurin sai ya ga yadda ake kashe mutane kamar ba gaskiya bani.

Abubakar ya ce an kashe yayansa 5 a rikicin. Ya kara da cewa yayansa basa cikin wannan fadar gaba daya, maganar bata shafesu ba, amma gashi yanzu an bar masa marayu 18 da zai dauki nauyin kula da su.

Daily Trust ta bayyana cewa ya zuwa yanzu dai hukumar SEMA ta bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa ta bada buhun shinkafa 25 da kudade naira 500,000 ga wadanda abin ya shafa. Sannan hukumar SEMA ta jihar jigawa ta bayyna cewa matsalar ta taso ne saboda satan da wasu mutane wadanda ba’a sansu ba har yanzun.

Dr Haruna Maigari shugaban SEMA  ya bayyana cewa, abin sata ne kuma an bi sawon barayin har zuwa wata rugar Fulani, wanda ya jawo tashin hankali har ya kai ga kashe-kashen mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments