Iran Da E3 Suna Ci Gaba Da Tattaunawa Kafin Taron JCPOA Na Gaba A Birnin Geneva

Wani jami’in kungiyar tarayyar Turai wanda baya son a fadi sunansa, yace kungiyar tana ci gaba da tattaunawa da Iran kan shirin Nukliyar kasar kafin

Wani jami’in kungiyar tarayyar Turai wanda baya son a fadi sunansa, yace kungiyar tana ci gaba da tattaunawa da Iran kan shirin Nukliyar kasar kafin taron yarjeniyar JCPO wanda za’a gudanar a nan gaba a birnin Geneva na kasar Austria.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazen GharibAbabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran shari’a da kuma al-amuran kasa da kasa yana fadar haka shi ma. Ya ce za’a gudanar da taron ne a matakin mataimakan ministocin harkokin waje na kasashen E3 wato Faransa, Ingila da kuma Jamus a bangare guda da kuma Iran. Gharibabadi ya kara da cewa, za’a gudanar da taron ne a ranar litinin 13 ga watan Jenerun da muke ciki a birnin Geneva.

Manufar taron ita ce, bitan al-amuran shirin nukliyar kasar Iran , sannan a halin yanzu bazamu iya fadar abinda taron zai haifar ba.

Gharib Abadi ya kara da cewa Iran tana halattan tarurrukan ne don kare hakkin mutanen kasar Iran. Ya kuma kammala da cewa wasu suna ganin taro mai zuwa yana iya zama masomin sake farfado da yarjeniyar JCPOA. Ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments