Kasashe Da Dama Suna Tuntubar Iran Kafin Shigewa Ta Mashigar Hormuz

Jami’in Iran ya bayyana cewa: Kasashe da dama suna tuntubar Iran game da wucewa ta mashigar ruwan Hormuz Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kan Harkokin

Hoton jiragen ruwa

Jami’in Iran ya bayyana cewa: Kasashe da dama suna tuntubar Iran game da wucewa ta mashigar ruwan Hormuz

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kan Harkokin Diflomasiyya na Tattalin Arziki Hamid Ghanbari ya bayyana cewa: Kasashe daban-daban suna yin mu’amala akai-akai da Iran don neman amincewarta kan jiragen ruwansu su ratsa ta Mashigar ruwan Hormuz.

Ghanbari ya bayyana cewa: “Kasashe daban-daban, ta hanyar wasiku da sakonni, suna neman izini cikin gaggawa da nuna damuwa ga jiragen ruwansu da zasu ratsa ta Mashigar ruwan  Hormuz.”

Fira Ministan Japan ya bayyana a baya cewa shi da kansa ya tuntubi Shugaban Iran Pezeshkian don neman izinin jiragen ruwan Japan su ratsa ta Mashigar ruwan Hormuz kuma ya gabatar masa da batun.

Jigilar jiragen ruwan kaya ta Mashigar ruwan Hormuz sun ragu da rabi a wannan watan idan aka kwatanta da watan da ya gabata, lokacin da yakin ke kara kamari. Jiragen ruwa da suka sami izini daga Iran kuma suka ratsa ta hanyar da aka tsara da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Iran ta kafa a halin yanzu ana ba su izinin ratsawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted