Kasar Libiya Ta Shiga Sahun Masu Shigar Da Kara Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kasar Libiya ta bi sahun kasar Afirka ta Kudu a shigar da karar aiwatar da kisan kare dangi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Kotun

Kasar Libiya ta bi sahun kasar Afirka ta Kudu a shigar da karar aiwatar da kisan kare dangi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta sanar da cewa: Kasar Libiya ta nemi shiga cikin sahun kasar Afirka ta Kudu a karar  da ta shigar kan batun shari’ar zargin gwamnatin yahudawan sahayoniyya na karya yarjejeniyar hana gudanar da kisan kare dangi kan wata al’umma.

A yammacin jiya Juma’a ne Majalisar Shugabancin kasar Libiya ta fitar da sanarwar cewa: Gwamnatin Libiya ta mika bukata ga Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa kan shigar da ita cikin sahun kasar Afirka ta Kudu da ke zargin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da aiwatar da kisan kiyashi a Zirin Gaza.

Abin lura a nan shi ne cewa kasashe da dama sun gabatar da bukatunsu na shiga cikin shari’ar, ciki har da Turkiya, Nicaraguwa da Colombiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments