Mataimakin Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jadadda cewa: Iran tana da karfin tabbatar da tsaron yankin
Mataimakin Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran (wato Majalisar Dokokin kasar), Hamid Ridha Hajji Baba’i, ya bayyana cewa: Iran ita ce kasa mafi ƙarfi a yankin, yana mai jaddada cewa, ƙasar da ke da ikon tabbatar da tsaron yankin ba Amurka ba.
Hajji Baba’i ya ƙara da cewa, a lokacin wani taro da aka yi a Lardin Zanjan da ke arewa maso yammacin kasar Iran a ranar Asabar da ta gabata, bai kamata ƙasashen yankin su dogara ga ƙasashen waje ba, sai dai ya wajaba su canza ra’ayinsu su koma ga al’ummar musulmi ‘yan uwansu.
Hajji Baba’i ya jaddada cewa: Yaƙi bai ƙare ba, amma ya ci gaba da gudana cikin matsin lamba ta hanyar takunkumin abokan gaba, matakan tattalin arziki, da siyasa a cikin duniyar gaske da ta kama-karya, yana mai cewa: “Tattaunawa ba ta nufin cimma yarjejeniya, maimakon haka, dole ne al’ummar Iran su ɗora buƙatunsu kan maƙiya.”