Khatibzadeh: Iran ba za ta amince da saryar da hakkokinta ba a duk wata tattaunawa da Amurka

Mashawarcin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Za su koma shawarwari da Amurka ne yayin da suke dauke da makamai a hannu Mai baiwa

Mashawarcin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Za su koma shawarwari da Amurka ne yayin da suke dauke da makamai a hannu

Mai baiwa ministan harkokin wajen Iran shawara Sa’ed Khatibzadeh, ya jaddada cewa: Iran ba za ta sake amincewa da Amurka kan duk wata tattaunawa da za ta iya yi ba, yana mai cewa makomar yankin ba kamar yadda Amurka da Isra’ila suke zato ba.

A ziyararsa ta farko da ya kai kasar China bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Iran a baya-bayan nan, Khatibzadeh ya yi wata fitacciyar hira da gidan talabijin na Phoenix, inda ya tattauna muhimman batutuwa da suka hada da ci gaban Shirin makamashin nukiliyar Iran, dangantakar shiyya da kasa da kasa, da makomar shawarwari, da dambaruwar yankin, da kuma yiwuwar barkewar wani babban rikici.

Khatibzadeh ya yi ishara da manufofin gwamnatocin Amurka da yahudawan sahayoniyya yana mai cewa: A kodayaushe ana samun karuwar tashin hankali, musamman ma a yayin da bangaren da ke adawa da gwamnatin Amurka da yahudawan sahayoniyya suke, Iran a kodayaushe tana neman zaman lafiya kuma ba ta kaddamar da wani yaki ba tsawon karnonin da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted