Guinea Ta Saki Sojojin Sierra Leon 16 Da Ta Kama

A wani yunkuri na kawo karshen sabanin kan iyaka, kasar Guinea ta saki sojojin kasar Saliyo 16 da ta kama, a farkon makon da ya

A wani yunkuri na kawo karshen sabanin kan iyaka, kasar Guinea ta saki sojojin kasar Saliyo 16 da ta kama, a farkon makon da ya kare.

A jiya Juma’a ne dai mahukuntan kasar Saliyo su ka sanar da cewa, makwabciyar tasu Guinea ta sakar mata sojoji 16 da ta kama da kuma wani jami’in dan sanda daya.

Ma’aikatar watsa labaru ta kasar Saliyo ta sanar da cewa; An mika dukkanin jami’an tsaron da aka kama, ga Saliyo.”

Tun da fari, ma’aikatar tsaron kasar Guinea ta ce, A ranar Lahadi  sojojin Saliyo sun shiga gundumar Koudaye akan iyakar faranah ba tare da an ba su izini ba, sannan kuma su ka kafa wani  tanti da daga tutar kasarsu.”

Sanarwar ma’aikatar tsaron kasar ta Guinea ta ce, sojojin na Saliyo sun yi kutse da zurfin kilo mita 1.4 a cikin kasar da ba tasu ba, don haka an kwace dukkanin kayan da suke a tare da su, kuma tuni an bude bincike domin gano abinda yake faruwa.

Ita kuwa kasar saliyo ta bayyana cewa; Sojojin nata suna kafa wata wani zango ne da kayan aiki a kan iyaka ta  Kalieyere a gundumar gundunar Falaba, da kasar Saliyo ce.” Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa, sojojin suna cikin wannan aikin ne sojojin Guinea su ka tsallako kan iyaka zuwa inda sojojin nasu suke, su ka yi awon gaba dasu.

Sabanin kan iyaka a tsakanin kasashen biyu ya samo ne tun a 1992-2002 da aka yi yakin basasa. A wancan lokacin kasar Guinea ta aike da sojoji domin su taimaka wajen fada da ‘yan tawaye, to amma bayan kare yankin ba su janye ba, sun ci gaba da zama inda suke.

Tun daga wancan lokacin ne ake samun sabani a tsakanin kasashen biyu, musamman akan yankin Yenga mai arzikin Lu’u’lu’u.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted