Search
Close this search box.

Kasar Cuba Ta Shiga Cikin Masu Kai HKI Kara A Kotun Manyan laifuka Ta Duniya Akan Gaza

Kasar ta Cuba ta sanar da cewa ta dauki matakin yin tarayya da kasar Afirka ta kudu wajen daukar matakan shari’a a kotun manyan laifuka

Kasar ta Cuba ta sanar da cewa ta dauki matakin yin tarayya da kasar Afirka ta kudu wajen daukar matakan shari’a a kotun manyan laifuka dangane da laifukan yaki da HKI take tafkawa a Gaza.

Tun a ranar juma’ar da ta gabata ne dai ministan harkokin wajen Cuba ya sanar da cewa, kasar tasa za ta shiga cikin sahun masu daukar matakan shari’a akan HKI saboda abinda take yi a Gaza.

Sanarwar ta ce, manufar daukar wannan matakin shi ne yadda za a kawo karshen laifukan da Isra’ila take tafkawa akan Falasdinawa.

A raanr 29 ga watan Disamba na 2023 ne dai kasar Afirka Ta Kudu ta kai karar HKI a gaban kotun ta duniya tare da kawo dalilai akan yadda yake yi wa Falasdianwa kisan kiyashi, tun daga 1948 har zuwa yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments