A wani taron manema Labarai a nan birninTehran, kakakin sojojin kasa na dakarun IRGC a nan JMI, Burgediya Janar Ali Muhammad Naeini ya fadawa yan jaridu cewa, tsaron JMI da kuma makamanta baa bin tattaunawa ne da makiya ba. Ya kuma kara da cewa, tsaron kasar Iran jan layi ne, haka ma, karfin sojojin kasar.
Janar Naeini ya ka ra da cewa, rawar dajin da sojojin IRGC suka yi a baya-bayan nan ya na tabbatar da hakan.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, Burgediya Janar Naeini yana maida martani ne ga gwamnatin Amurka wace ta fara maganar cewa, zata tattauna da kasar ta Iran ne a kan shirinta na makamai masu linzami, da kuma shirin ta na makamashin nukliya.
Kakakin sojojin ya bayyana cewa a dai dai lokacinda JMI take amfani da diblomasiyya a dayan bangaren kuma ta na da makamanta a kan teburi idan har diblomasiyya ta kasa kai kasar ga zaman lafiya da makiya zata yi amfani da su.
Kafin haka dai jakadan Amurka na musamman a gabas ta tsakiya, Steve Witkoff ya fadawa tashar talabijin ta Fox news ta kasar Amurkan kan cewa a tattaunawar da ya fara da jami’an gwamnatin kasar Iran, yana fatan zasu tattauna kan shirinta na makamashin Uranium da kuma, yiyuwar ta kera makaman nukliya, har’ila yau da kuma tarin makamai masu linzami da take da su.
Kakakin dakarun na IRGC ya ce hare-haren wa’adus Sadik na daya da na biyu, kekyawar misali ne na nuna karfin makaman linzami na kasar, sannan mutanen kasar suna goyon bayan gwamnati a kan mallakar wadannan makamai.