Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa babu batun tattaunawa kan shirin kasar na tace sinadarin Uranium wanda ke a matsayin wani bangare na shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya. Abbas Araghchi ya kuma ce tattaunawar Tehran da Washington ba za ta haifar da wani sakamako ba idan ana amfani da matsin mata lamba da […]

Ministan harkokin wajen Najeriya Ya kai ziyara Nijar

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata ziyarar aiki zuwa makobciyuar kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan it ace ziyara irinta ta farko da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai a Jamhuriyar Nijar tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka kifar da mulkin farar hula na Mohamed Bazoum a watan Yulin […]

‘Yan tawayen Sudan sun kafa tasu gwamnati

kwamandan RSF

Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar. Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur. Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da […]

Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka

Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su […]

A Kalla Mutane 9 Ne Su Ka Yi Shahada A Gaza

HKI tana ci gaba da kai wa yankunan Gaza mabanbanta hare-hare da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai a yau Laraba. Tun da safiyar yau Laraba ne HKI ta kai hari akan wani gida dake unguwar “al-Tuffah” dake cikin birnin Gaza da hakan ya sa mutane 6 su ka yi shahada. A yankin Jabaliya kuwa […]

Yadiot Ahranot: Amurka Ta Bayyana Lokacin Ficewarta Daga Syria

Jaridar “Yadiot-Ahranot” ta rubuta cewa, jami’an Amurka sun sanar da sojojin Isra’ila a lokacin da za ta janye sojojinta daga kasar Syria. Jaridar ta ce, jami’an tsaron kasar ta Amurka sun fada wa sojojin Isra’ila cewa, janye sojojin nata zai fara ne nan da watanni biyu masu zuwa. Rahoton jaridar ta ‘yan sahayoniya ya ce, […]

 ‘Yan Hamayyar Tanzaniya Sun Ki Amincewa Da Hana Su Shiga Zabe

Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba. Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da […]

Amurka Tana Shirin Mikawa HKI Dubban Boma-Bomai Cikin Makonni Masu Zuwa

Gwamnatin Amurka ta amince da shirin mikawa HKI dubban boma-bomai saboda kashe falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sojojin HKI suna jiran isowar boma-bomai daga kasar Amurka don fara wani aikin soje na musamman a Gaza. Saboda kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Wata majiyar HKI, yahudawa ta […]

Hamas: Yahudawan Da Ake Tsare Da Su A Gaza Za Su Koma A Cikin Makara

Reshen soja na kungiyar Hamas wato rundunar Izzuddin Qassam, ya gargadi iyalan fursinonin yahudawan Sahyoniyya wadanda take tsare da su a Gaza kan cewa yayansu zasu koma hannunsu gawaki, saboda irin yadda HKI take kara yawaita Jefa boma-boman a kan Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto  wani mai magana […]

IRGC: Butun Tsaron Iran Da Karfin Sojojinta Ba Abin Tattaunawa Da Makiya Ba

A wani taron manema Labarai a nan birninTehran, kakakin sojojin kasa na dakarun IRGC a nan JMI,  Burgediya Janar Ali Muhammad Naeini ya fadawa yan jaridu cewa, tsaron JMI da kuma makamanta baa bin tattaunawa ne da makiya ba. Ya kuma kara da cewa, tsaron kasar Iran jan layi ne,  haka ma, karfin sojojin kasar. […]

An Gudanar Da Taron Kasa da Kasa Don Tallafawa Yan Gudun Hijira Na Sudan

Jami’an diblomasiyya daga kasashen duniya da dama, da kuma wakilan kungiyoyin agaji daban-daban sun hadu a birnin London na kasar Burtania don tattauna batun yakin da ke faruwa a kasar Sudan wanda a halin yanzu yake cika shekaru 2 ke nan. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika New” ya bayyana cewa, taron na kwana guda […]