Financial Times: Trump Ya Shiga Rudani Game Da Yaki Da Iran

Jaridar Financial Times ta Birtaniya ta buga labarin cewa: Shugaban Amurka Trump ya shiga rudani game da yaki da Iran Jaridar Financial Times ta Birtaniya

Jaridar Financial Times ta Birtaniya ta buga labarin cewa: Shugaban Amurka Trump ya shiga rudani game da yaki da Iran

Jaridar Financial Times ta Birtaniya ta ruwaito cewa: Shugaban Amurka Donald Trump yana cikin tsaka-tsaki tsakanin ƙara ta’azzara rikici da Iran da kuma amincewa da yarjejeniyar bisa sharuɗɗan Iran, tare da ƙarancin zaɓuɓɓuka don ficewa daga yaƙin da ya yi iƙirarin zai ƙare da “miƙa wuyar Jamhuriyar Musulunci ta  Iran”.

Jaridar, tana mai nuni ga tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da Oman, ta rubuta cewa idan waɗannan tattaunawar suka haifar da yarjejeniya, sakamakon zai zama babban bambanci daga manufofin farko da Trump ya sanar lokacin da ya fara yaƙi da Iran.

A cewar jaridar Financial Times, buƙatun gwamnatin Amurka ga Iran, daga buƙatu iri-iri da suka haɗa da iyakance shirin makamashin nukiliyarta, dakatar da samar da makamai masu linzami na ballistic da kuma kawo ƙarshen goyon baya ga ƙungiyoyin gwagwarmaya da ke take kawance da su, a halin yanzu an rage su zuwa buƙata ɗaya ta gaggawa: mayar da Mashigar Hormuz zuwa yanayin da yake ciki kafin yaƙi.

Jaridar ta ambato Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio yana cewa: “Hana Iran mallakar makamin nukiliya shine yarjejeniyar ƙarshe da Amurka ke son cimma da Iran, amma yarjejeniyar nan take da kuma batun da aka fi mayar da hankali a kai yanzu ita ce Mashigar ruwan Hormuz.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted