Jaridar Birtaniya Ta Ce Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Za Ta Iya Rusa Kungiyar Hamas Ba

Jaridar Birtaniya ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba zata iya rusa kungiyar Hamas ba Jaridar “The Times” ta kasar Birtaniya ta buga wani

Jaridar Birtaniya ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba zata iya rusa kungiyar Hamas ba

Jaridar “The Times” ta kasar Birtaniya ta buga wani bincike da ya yi tsokaci kan gazawar gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya na cimma burukan da ta ayyana cikin manufofinta na rusa abin da ta kira tushen ta’addanci a Zirin Gaza ta hanyar kawar da yunkurin “kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas.

Binciken wanda mai bincike kan al’amuran Gabas ta Tsakiya Beverly Milton Edwards ta rubuta, ya yi nuni da cewa har yanzu gwagwarmayar Falasdinawa tana tsaye da kafafunta, kuma ana sa ran za ta ci gaba da janyo hasara wa rundunar sojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila duk da kwashe tsawo fiye da kwanaki 220 tana kaddamar da hare-hare kan Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments