Search
Close this search box.

Jami’an Tsaron Kan Iyaka Sun Kashe Yan Ta’adda 2 Sun Kuma Kama Wani A Lardin Sistan Baluchestan

Jami’an tsaro na kan iyaka a nan Iran sun bada sanarwan kashe yayan wata kungiyar yan ta’adda guda biyu a lardin Sistan Baluchestan a yaum

Jami’an tsaro na kan iyaka a nan Iran sun bada sanarwan kashe yayan wata kungiyar yan ta’adda guda biyu a lardin Sistan Baluchestan a yaum Asabar, sun kuma kama wani guda da ransa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Burgediya Janar Akhmad Ali Gudarzi shugaban jami’an tsaron kan iyakokin kkasar yana fadar haka a yau Asabar.

Ya kuma kara da cewa, ma’aikatansa wadanda suke aiki dab da kan iyakar kasar da kasar Pakistan sun ga lokacinda yan ta’addan daga wata kungiya masu kafirta musulmi mai suna –Ansarul-Furkan’ suke tsallaka kan iyakokin kasashen biyu daga kasar Pakistan.

Don haka basu yi wata wata suka tsaresu, amma sun nuna turjiya wanda ya kai ga musayar wuta a tsakaninsu, idan daga karshe an kashe yan ta’addan guda biyu sannan suka kama guda daga cikinsu.

Banda haka jami’anm tsaron kan iyakar sun sami makamai tare day an ta’addan sun kuma kwacesu.

Mayakan yayan wannan kungiyar dai sun sha shiga cikin kasar Iran daga kasar Pakistan su kuma kashe jami’an tsaron JMI a duk sanda suka sami damar yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments