Jami’an Lebanon sun yi marawa Hizbullah baya kan shishigin Isra’ila a Lebanon

Jami’ai da shugabannin jam’iyyun siyasa na Lebanon da dama  sun yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a yankin kudancin birnin Beirut, a

Jami’ai da shugabannin jam’iyyun siyasa na Lebanon da dama  sun yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a yankin kudancin birnin Beirut, a daidai lokacin da firaministan rikon kwarya Najib Mikati ya bayyana cewa, Lebanon za ta ci gaba da rike cikakken ‘yancinta na dakile cin zarafi na Isra’ila.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta bayar da rahoto a ranar Talata cewa harin da Isra’ila ta kai kan wani gini da ke unguwar  Haret Hreik a kudancin birnin Beirut, ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 3 tare da jikkata wasu 74.

Firaministan na Labanon ya ce, kasarsa za ta gabatar da wanann batu na ta’addancin Isra’ila a kan Lebanon, wanda dole ne al’ummomin duniya  su yi iyakacin kokarinsu don tilastawa Isra’ila kiyaye ka’idoji da dokoki na kasa da kasa.

Mikati ya kara da cewa “Za mu rike cikakken ‘yancinmu na daukar dukkan matakan dakile ta’addancin Isra’ila.”

Ministan harkokin wajen kasar Labanon Abdallah Bou Habib, ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters, inda ya bayyana cewa, Lebanon na shirin shigar da kara ga MDD.

Bou Habib ya yi fatan mayar da martani daga bangaren Hizbullah  game da ta’asar Isra’ila, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments