A yau ne Jamhuriyar Nijar ke bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar kasar Faransa.
Shekaru 64 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Augustan-1960M. Jumhuriyar Nijar da ke yammacin nahiyar Afrika ta sami ‘yancin kanta daga mulkin mallakar turawan Faransa, wadanda suka fara shiga kasar tun a cikin karni na 15 miladiyya. Amma a shekara ta 1922 suka mayar da kasar karkashin mulkin mallakarsu.
Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacin da mutanen kasar suka fara gwagwarmayan neman ‘yancin kansu wanda ya tabbata a rana irin ta yau.
Jumhuriyar Nijar tana daga cikin kasashen Afirka mafi girma ta fuskacin fadin kasa, wanda ya kai kilomita murabba’i 1,267,000. Kuma tana makwabtaka da kasashen Benin, Libya, Chadi, Nigeriya, Algeria, Burkina Faso da kuma Mali.
Jamhuriyar Nijar na da arziki na albarkatun kasa masu tarin yawa, da suka hada da zinariya, danyen man fetur, karfen uranium, da dai sauransu, a daya bangaren kuma tana da arzikin noma da kiwo.