Jagoran Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ya Ce: Dakarunsa Zasu Ci Gaba Da Yaki Da Isra’ila

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada ci gaba da gwagwarmaya soji kan makiya ‘yan mamayar Isra’ila Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada ci gaba da gwagwarmaya soji kan makiya ‘yan mamayar Isra’ila

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Tafarkin al’ummar Yemen na goyon bayan al’ummar Falastinu yana ci gaba kuma tabbatacce kuma yana kara ruruwa.

A cikin jawabinsa Sayyed al-Houthi ya ce: ‘Yan kasar Yemen suna fuskantar makiya a dukkan fagage: ta fuskar siyasa, soja, tattalin arziki da kuma ta kafofin watsa labarai, ba za su yi rauni ba sakamakon wuce gona da iri da ake yi kan su.

Ya kara da cewa al’ummar kasar Yemen suna yin jawabi da ya hau kansu wajen taimakawa wa al’ummar Falastinu, yana mai bayyana cewa; Suna tare da Falasdinawa kuma suna goyon bayan su. Ya kuma jaddada cewa; Matsayin kasar Yemen tabbatacce ne wajen goyon bayan al’ummar Falasdinu, kuma ba zai yi kasa a gwiwa ba, ko da kuwa zai ci gaba da fuskantar irin kalubalen da yake fuskanta.

Dangane da shahadar fira ministan gwamnatin canji da gine-gine da kuma mukarrabansa, Sayyed al-Houthi ya mika ta’aziyyarsa ga dukkan iyalai da ‘yan uwan ​​shahidan, da dukkan mukarrabansu na hukumomin gwamnati, da kuma al’ummar kasa masoya, domin su ne shahidan daukacin kasar Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted