Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Matsayin Iran Na Goyon Bayan Gwagwarmaya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da matsayin Jamhuriyar Musulunci mai cike da goyon bayan ‘yan gwagwarmaya Dangane da ƙa’idar hana kai hari da

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da matsayin Jamhuriyar Musulunci mai cike da goyon bayan ‘yan gwagwarmaya

Dangane da ƙa’idar hana kai hari da kuma ƙarfafa ƙa’idar ɗaukar fansa, Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wuraren soji a arewacin Falasɗinu da Isra’ila ta mamaye, don mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da hare-haren da Isra’ila take kai wa kan birnin Beirut da yankunan kudancin Lebanon. Wannan aikin ya nuna tabbacin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Mojtaba Khamenei, na goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ga gwagwarmayar da take yi kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Ali Akbar Velayati, mai ba da shawara kan harkokin ƙasa da ƙasa ga Jagoran, ya tabbatar da cewa: Wauta da maƙiya suka yi wajen kai hari kan birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon ya haifar da matakin farko na martanin Iran, yana mai jaddada cewa: ‘Yan gwagwarmaya suna da ikon rufe mashigar ruwan Hormuz da mashigar ruwan Bab el-Mandeb.

A halin yanzu, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi gargaɗi game da cikakken martani mai ƙarfi ga duk wani sabon hari da aka kai wa Lebanon ko Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted