Jagoran dakarun kai daukin gaggawa na Sudan ya bayyana matsayinsa na amincewa da shiga tattaunawar kasar Switzerland kan rikicin kasarsa
Kwamandan rundunar dakarun kai daukin gaggawa a Sudan, Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), ya sanar da amincewarsa da bukatar tsagaita bude wuta a Sudan.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na dandalin “X”, Hemedti ya ce ya yi maraba da gayyatar da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi masa na shiga zaman shawarwari kan rikicin Sudan da yake neman rusa kasar.
Dagalo ya rubuta cewa: Ya amince da shiga zaman tattaunawan tsagaita bude wuta a Sudan da za a gudanar a ranar 14 ga Agusta mai zuwa na wannan shekara a kasar Switzerland.
A nata bangaren, Amurka ta yi kira ga sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da su shiga zaman gudanar da shawarwarin zaman lafiya da za a gudanar a watan Agusta mai zuwa a kasar Switzerland da nufin kawo karshen rikicin Sudan. Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana cewa: Amurka ta gayyaci sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces don shiga tattaunawar tsagaita bude wuta, da Amurka za ta kasance mai shiga tsakani, da za a fara ranar 14 ga watan Agusta a kasar Switzerland.