Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Gungun Mabarnata Ne Masu Aikata Muggan Laifuka

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yahudawan Sahayoniyya a matsayin wasu gungun masu aikata muggan laifukan kashe-kashen rayuka kuma ‘yan ta’adda Jagoran juyin juya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yahudawan Sahayoniyya a matsayin wasu gungun masu aikata muggan laifukan kashe-kashen rayuka kuma ‘yan ta’adda

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne sabuwar gwamnatin Iran ta kasance mai tasiri da rawar da take takawa dangane da batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa, yana mai nanata cewa: Batun Gaza ya zama ruwan dare gama duniya, kuma har yanzu shi ne batun farko na duniyar Musulunci.

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin rantsar da zababben shugaban kasar Iran a jiya Lahadin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da cewa: Yahudawan sahayoniyya wasu gungun ‘yan ta’adda ne na masu aiwatar da kashe-kashen gilla da ayyukan ta’adda tare da bullo da wani sabon tarihi na aikata muggan laifuka ta hanyar kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Ya kara da cewa: Abin kunya shi ne ‘yan majalisar dokokin Amurka sun zauna suna sauraran kalaman mutumin da ke shugabantan wannan gungun ‘yan ta’adda.

Jagoran ya fara jawabin nasa ne da yin nazari a kan yadda ake gudanar da mulki a Iran da kuma zabukan da suka gabata, daga nan sai ya bayyana jawabin shugaban kasar Masoud Pezeshkian a matsayin bayananne, mai zurfi, mai nuni da sadaukar da kai ga hakikanin manufofin Musulunci na jagorancin al’ummar musulmi.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments