Jagoran juyin musuluncin na Iran Ayatulah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa, kungiyoyin gwgawarmaya suna kara karfi a kowace rana.
Wannan bangaren na jawabin jagoran juyin musulunci ne dai Fira minstan HKI Benmjamine Netenyahu ya sa ashafinsa na “X” a karkashin jawabinsa ga Majalisar dokokin Amurka.
Ayatullah sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Duk da cewa wata kasa mai karfin soja da tattalin arziki da girman tasirin sitasa, kamar Amurka tana goyon bayan ‘Yan Sahayoniya, amma har yanzu sun kasa durkusar da Hamas.