Tsohon kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Mohammad Ali Ja’afari, ya bayyana cewa: Iran ba ta da wani takunkumi kan adadin makamai masu linzami, kuma wannan karfin ya hada da nau’ikan makamai masu linzami daban-daban masu cin iyakoki daban-daban. Ya kara da cewa: Karfin kasar a wannan fanni yana da fadi kuma ba shi da iyaka.
A wata hira da manema labarai da aka watsa jiya, Asabar, Manjo Janar Ja’afari ya yi magana kan batutuwan yanki, na kasa da kasa, da na cikin gida, ciki har da ci gaba kan bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma halin da ake ciki a Lebanon da Hezbollah, yana mai cewa: “Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce, gwagwarmaya ba wani abu ne na zahiri da za a iya kayar da shi ba. Da ace gwagwarmaya wata abu ce na zahiri, da Hezbullah ba za ta wanzu har zuwa yau ba.”
Ya kara da cewa: “Duk da mummunan matsin lamba da Hezbullah ta sha, gami da hasarar manyan shugabanninta, har yanzu tana kan tafarkin gwagwarmaya. Makiya za su iya kai hari kusan kashi 30% na karfin Hezbullah, amma kashi 70% na wadannan karfin sun kasance a shirye, kuma wannan a cikin kansa shaida ce ta zurfin da karfin gwagwarmaya.”