Bayanai daga Isra’ila ne cewa Jami’an gwamnatin kasar na kalubalantar yadda shugaba Donald trump, na Amurka ke son cimma yarjejeniya da Iran ”ko ta halin ka kaka”.
Gidan talabijin na Isra’ila Channel 12 ya ce jam’ian sun nuna shakku kan sabon kokarin diflomasiyya na Amurka da Iran, suna korafi kan yadda Trump da masu ba shi shawara ke son cimma yarjejeniya da Iran “ko ta halin kaka”.
A cewar rahoton, Washington ba ta yi wa Isra’ila bayani kai tsaye kan tattaunawar da ta yi da Iran game da mashigar Hormuz ba, wanda hakan ya bar hukumomin Isra’ila cikin duhu.
Channel 12 ta ruwaito cewa jami’an Isra’ila na cewa da za a iya cimma daidaito kan mashigin Hormoz da kuma share fagen Washington da Tehran su koma kan yarjeejniyar fahimtar juna da suka cimma a baya.
Tun da farko a ranar Talata, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce Washington da Tehran har yanzu ba su kammala tattaunawa kan yadda za su bi ta hanyoyin ruwan na duniya masu muhimmanci ba, amma yana fatan za’a cimma yarjejeniya “nan ba da jimawa ba.”
Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta a watan Afrilu sannan daga baya suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Pakistan ta shiga tsakani a watan Yuni da nufin kawo karshen rikicin soja da kuma cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.
Duk da haka, yarjejeniyar ta ruguje a watan da ya gabata inda bangarorin biyu suka yi musayar hare-hare na kusan makonni biyu kafin Trump ya dakatar da kai hare-haren ba zato ba tsammani a yayin da ake samun rahotannin tattaunawa don warware rikicin.