Isra’ila Ta Kashe Yara Guda 2  Sakamakon Hari A Yankin Gaza

Sojojin Isra’ila sun kai sabbin hare-hare a Zirin Gaza, inda aka kashe yara biyu tare da jikkata wasu Falasdinawa, duk da yarjejeniyar dakatar da bude

A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da isra’ila ke yi ta kaddamar da wasu hare-hare yankin gaza kuma ta kashe wasu yara guda biyu tare da jikkata wasu na dabam, inda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta ce daga lokacin da aka dakatar da bude wuta zuwa yanzu akalla falasdinawa 1257 ne suka yi shahada

ko a ranar Asabar ba sojojin mamaya na isra’ila sun kai hare-hare a Gaza kuma sun kashe tare da jikkata falasdinawa duk da kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta da ta yi da kungiyar Hamas.

gidan talabijin din almayadeen ya nakalto cewa wani bafalasdine ya mutu bayan da sojojin isra’ila suka bude masa wuta a deir al-balah dake tsakiyar gaza, haka shi ma wani yaro ya jikkata bayan da sojojin isra’ila su kai hari a layin  yafa dake altuffa mai makwabtaka da gabashin gaza

haka zalika wata yarinya yar shekara 13 ta jikkata bayan da sojojin isra’ila suka bude mata wuta a kudancin khan yunus dake kudancin zirin Gaza, suma wasu guda 4 sun jikkata, halin da wasu ke ciki yayi muni sosai bayan da tankokin yaki isra’ila suka kai kai hari a kusa da wata babban hanya a yankin al-mawasi a khan yunus.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted