Iran: Amurka Da HKI Suna Son Hada Iran Fada Da Makobtanta

Shugaban Iran, Dr Masoud Pezeshkian, ya ce Amurka da HKI suna kokarin haddasa gaba tsakanin Iran da makwabtanta, yana mai cewa Tehran na son warware

Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa HKI da Amurka suna son cusa gaba da kiyayya tsakanin Iran da makobtanta bayan ta kasa samun nasara a kanta a yankin ta take fafatawa da ita.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Pezeshkiyan yana fadar haka ajiya Jumma’a a wata tashar talabijan ta kasa. Ya kuma kara da cewa, Iran ta sami nasarar warware wasu matsaloli tsakaninta da kasashen larabawa na yankin tekun farisa.

Ya kara da cewa Amurka ta hana gwamnatin kasar Faransa aiwatar da wani fahintar juna da suka cimma da kasar Faransa dangane da dage mata takunkuman ‘Snapback’ wanda kuma ya nuna cewa kasashen turai basa da yencin a cikin al-amura da dama a harkokinsu na kasashen waje.

Ya ce, bata fara yakin da Amurka da HKI suka dora mata ba, kuma tana kare kanta ne, kuma dole ta yi haka, sannan zata ci gaba da hakan da cikekken karfinta da kuma hadin kan mutanen kasar.

Ya kammala da cewa Iran bata nema yaki ba, kuma a duk lokacinda ta ga cewa zata sami hakkinta ta hanyar diblomasiyya ba zata ci gaba da yaki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted