Kasashen AES Sun Kalubalanci Kalaman Tinubu Kan Tsaro

Da yake magana a madadin takwarorinsa daga Mali da Nijar, Ministan Harkokin Wajen Burkina ya bayyana wannan da abin mamaki

Kasashen kawancen Sahel na AES, sun kalubalanci kalamman baya baya nan na shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na cewa matsalor a kasarsa ta ta’aka ne da matsalolin da kasashen ke fama da dasu.

Kalamman sun janyo tsamin dangantar diflomasiyya tsakanin kasashen uku Nijar, Mali da Burkina Faso da kuma Tarayyar Najeriya biyo bayan kallaman da Shugaba Tinubu ya yi, wanda jami’an diflomasiyyar kasashen kawancen suka bayyana a matsayin “masu sauri, kuma abin mamaki.”

Wakilai daga Burkina Faso, Mali, da Nijar sun gana da jami’in diflomatiyar Najeriya a Ouagadougou don bayyana “bacin ran ” kasashen Sahel Alliance game da kalaman da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi a ranar 30 ga Yuli, a lokacin wani taro da shugabannin gargajiya na kasarsa, game da mastalar sace-sacen mutane da hare-haren ta’addanci a Najeriya.

Kamar yadda Ministan Harkokin Waje na Burkina Faso, Karamoko Jean Marie TraorĂ© ya ambato, shugaban kasar Najeriya ya yi ikirarin cewa yanayin tsaro ya faru ne sakamakon “rushewar” tsaro a kasashen Sahel makwabta, wanda ya taimaka wajen haifar da sace-sacen mutane da hare-haren ta’addanci a Najeriya.

“Wasu daga cikin [‘yan ta’adda] ba ‘yan Najeriya ba ne, Kun gani, matsalar rashin tsaro a Mali, Burkina Faso, da Nijar kawai tana kara ta’azzara matsalolinmu,” in ji Bola Tinubu.

Da yake magana a madadin takwarorinsa daga Mali da Nijar, Ministan Harkokin Wajen Burkinabe ya bayyana wannan da abin mamaki, yana bayyana son zuciya daga bangaren shugabannin Najeriya.”

A game da hakan, ya jaddada cewa kasashen AES ba sa neman takun tsaka na diflomasiyya, sun fi son ci gaba da tattaunawa ta “gaskiya, da girmamawa, a tsakanin kasashen da Najeriya.

Ya bukaci Abuja da ta inganta hadin kai maimakon yin amfani da kalaman batanci da ka iya haifar da rarrabuwar kawuna da kuma raunana hadin gwiwar yankin.

A nasa bangaren, jami’in hulda da jama’a na ofishin jakadancin Najeriya da ke Ouagadougou ya bayyana cewa ya lura da sakon da hukumomin AES suka aika masa kuma ya yi alkawarin isar da shi zuwa Abuja.

 Ya kuma yaba wa kokarin tsaro na kasashen ESA a yaki da ta’addanci, yana mai ambaton rawar da Nijar ke takawa wajen hana hare-hare da kan iya shafar wasu yankunan Najeriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted