IRGC Ta Yabawa Kafafen Yada Labarai Na Iran

Iran na bikin Ranar 'Yan Jarida a ranar 8 ga Agusta don tunawa da dan jarida Mahmoud Saremi, wanda aka kashe a Afghanistan a 1998.
Brig. Gen. Ahmad Vahidi l

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta yabawa kafafen yada labaran na kasar kan yadda suke yaki da gurbatatun bayanai da kuma da kuma labaren bogi na abokan gaba, tana mai jaddada cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye hadin kan kasa a lokacin rikice-rikicen da suka faru kwanan nan.

IRGC a ta bayyana hakan a yayin da ake bikin Ranar ‘Yan Jarida ta Iran, inda ta yabawa ‘yan jarida kan rawar da suka taka wajen sanar da jama’a, wayar da kan jama’a a lokacin kalubale.

Rundinar ta ce, amincewa da gazawar shugaban Amurka Donald Trump a yakin da ya yi da Iran ya samo asali ne daga kokarin da kafafen yada labaran juyin juya halin Iran suka yi na dakile gurbatatun bayanai na abokan gaba.

“A yau, yankin da duniya sun shaida daya daga cikin yake-yake mafi rikitarwa da sakamako a tarihin zamani,” in ji sanarwar, tana mai nuni da yake-yake na biyu da na uku da Amurka da Isra’ila suka yi kan Iran.

IRGC ta lura cewa duk da kokarin soja da kafofin watsa labarai na Washington da Isra’ila, sun kasa cimma manufofinsu, yayin da rikice-rikicen suka fallasa wani babban kalubale, rarrabuwar kawuna tsakanin kawayen kasashen yamma da kuma raguwar tasirinsu.

Sanarwar ta ce, “Kafafen yada labarai na duniya, wadanda suka amince da gazawar Washington na cin galaba a kan Jamhuriyar Musulunci, suna magana a fili game da “kayan da Trump ya sha da kuma ‘tarkon da ya kirkira da kansa’ a yakin da ya yi da Iran.”

Ya kara da cewa wasu rahotannin kafofin watsa labarai sun bayyana yarjejeniyoyin da aka cimma a matsayin ”mika wuya na Amurka” a gaban Iran.

IRGC ta yaba wa ‘yan jarida wadanda, a lokacin yakin da ya gabata, suka yi aiki don samar da rahotanni kan abubuwan da suka faru a kan lokaci, suka ba da rahoto kan kasa da hadin kan kasar da ba a taba gani ba.

Ta yaba wa ‘yan jarida waÉ—anda suka ci gaba da aikinsu duk da barazana da yanayi mai hadari, tana mai cewa wasu sun rasa rayukansu yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Iran na bikin Ranar ‘Yan Jarida a ranar 8 ga Agusta don tunawa da dan jarida Mahmoud Saremi, wanda aka kashe a Afghanistan a 1998.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted