Ibrahim musawi wani dan majalisa a kasar labanon kuma kusa a bangaren siyasa na kungiyar hizbullah ya dora alhakin dukkan yake yaken da ake yi a yammacin Asiya kan kasar Amurka ,kuma ya jaddada cewa kungiyar gwagarmaya ta hizbullah ba zata taba mika wuya ga matsin lamba ko wata barazana ba.
Yace Washington ce ke da alhakin yake-yake da rikici da yankinmu ke ciki, goyon bayan da Amurka ke bawa isra’ila shi ne babban abin da ya bata lasisi cin karenta babu babbaka a yankin,
Haka zalika ya soki gwamnatin kasar labanon kan gum da baki da take yi game da ci gaba da kai hare-hare da cin zarafin alummar kudancin kasar da isra’ila ke yi, kuma yayi watsi da tattaunawar gaba da gaba dake gudana tsakanin Berut da Tel aviv biyasa shiga tsakanin Amurka
Daga karshe yayi suka game da mataken da makiya na waje da wasu bangarorin siyasa a kasar labaon suke dauka kan kungiyar hizbullah, yace matsin lamba ko barazana da kuma yada farfagandar karya ba zai tilastawa hizbullah ta yi watsi da manufofi da tsarinta da ta yi imanu da su ba