Mohammad baqer zolqadr babban sakataren hukumar koli ta tsaron kasa ya jaddada cewa iran ba zata bude ko sassauta mataken da take dauka a mashigar Hurmuz ba har sai kasar Amurka ta canza halayen da take nunawa kasar Iran,
Iran ta sanya tsauraren matakai ne a mashigar Hurmuz tun bayan da kasar Amurka da HKI suka kaddamar da hari kan kasar iran a farkon watan maris , mashigar ruwan mai matukar muhimmanci da mafiyawancin makamashi da kashi 3 na takin zamani da duniya ke bukata suke wucewa ta wajen
Acikin sakon da ya aike da shi game da ranar yan jarida ta duniya ya bayyana sharudda guda 6 da iran ta gindaya kafin amincewa ta bude mashigar Hurmuz, wato dole ne amurka ta dakatar da cin zarafin abubuwan da alummar iran suka yi Imani da shi, kawo karshen duk wani hari kan iran da sauran kawayenta,
Har ila yau da kuma cire janye killacewar da tayi mata ta taku, da kuma cire sauran takunkumin da ta kakaba mata, da sakin dukkan kadarorinta da take rike da shi, da kuma biyan diyyar dukkan asarar da ta jawo mata a lokacin yake.
Daga karshe yace dukkan wadannan sharudda bukata ce da miliyoyin iraniyawa suka gabatar wadanda suka kasance a kan tituna domin nuna goyon bayansu ga gwamnatin musulunci tun lokacin da Amurka ta kaddamar da yaki kan kasar a ranar 28 ga watan Fabareru