A Jamhuriyar ana ci gaba da gudanar da bincike game da wani mummunan hatsarin motocin bas na sufurin al’umma da ya faru a ranar Juma’a, a kan hanyar Maradi-Madaoua.
Alkalumman wucin gadi sun nuna cewa mutane 21 ne suka rasa rayukansu a hatsarin, kana wasu 37 suna jinya a asibiti sakamakon samun rauni.
Gwamnan JIhar Tahoua, Kanar-Manjo Souleymane Amadou Moussa, tare da abokan aikinsa, sun je wurin da lamarin ya faru don isar da ta’aziyya ta manyan hukumomin kasar.
A cewar Gwamnan Tahoua, hatsari ne mai matukar tsanani, wanda ya haifar da mace-mace da raunuka.
A madadin hukumomi Nijar, ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da kuma kasar Nijar, kafin ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Gwamna Souleymane ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga masu amfani da hanya da su rika taka-tsantsan.
Ya kuma yi kira ga manajojin kamfanonin sufuri da su ci gaba da wayar da kan ma’aikatansu don hana wannan nau’in hatsari.
Bugu da kari, Gwamnan Tahoua ya yaba wa ma’aikatu na lafiya, da hukumomin gargajiya na Madaoua kan koĆ™arin da suka yi na ceto rayuka.
A cewar Kwamandan Bataliyar Jandarmerie na Madaoua, hatsarin ya shafi bas guda biyu guda da ke zuwa daga Maradi dauke da sojoji da kuma wata bas da ke zuwa daga Madaoua, yana mai bayyana cewa bas din biyu sun cin karo da juna da karfi.