Ministan harkokin wajen Burkina faso ya yi Allah wadai da kalaman da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 30 ga Yuli, wanda ya danganta rashin tsaron da ke faruwa a arewacin Najeriya da sakaci da rashin bayar da kulawa da ta dace daga kasashen Sahel makwabta.
Ƙasashen kawancen Sahel na AES da suka hada da Nijar ,Mali,Burkina Faso ta bakin ministan harkokin wajen Burkina Faso sun bayyana rashin gamsuwar su biyo bayan kalaman shugaban na Najeriya,da babbar murya Karamoko Jean-Marie Traoré ya na mai bayyana irin namijin kokarin da wadanan kasashe ke yi na ganin an kawo karshen ayukan ta’addanci,wanda wasu daga cikin masu fada a ji a Najeriya ke tallafawa ayukan ta’addanci, ministan ya bukaci Najeriya ta sake duba tsarin da take da shi a kai..
Kalaman na Ministan harkokin wajen Burkina Faso na zuwa ne bayan da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabanin gargajiya a ranar 30 ga watan yuli inda ya danganta wasu daga cikin matsaloli na tsaro da sace-sacen mutane a arewacin Najeriya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda daga kasashe makwabta.
Wannan ya sa Ministan harkokin waje na Burkina, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya fitar da wanan sanarwa mai dauke da sanya hannunsa.A cikin takardar, ya jaddada cewa ta’addanci barazana ce gama gari.
Ministan harkokin wajen ta Burkina Faso. da Wakilan kasashe uku na AES, wadanda suka yi taro a Ouagadougou, sun kira babban jami’in hulda da jama’a na Najeriya, suna yin Allah wadai da kalaman da Bola Ahmed Tinubu, waɗanda suka ɗauka a matsayin “ba daidai ba.” Ministan harkokin wajen Burkinabe ya tabbatar da cewa, ta hanyar kalamansa,