Shugaban Kasar Turkiyye Recep Tayyip Erdogan ya ce Yarjejeniyar Tsaron Makka da aka sanya wa hannu tsakanin Türkiye, Saudiyya da Pakistan ta shafi kowace kasa kuma a bude take ga sauran kasashe aminai da ke neman zaman lafiya, da kwanciyar hankali a yankin.
A cikin wani sako a dandalin sada zumunta, Erdogan ya ce yarjejeniyar, za ta karfafa hadin gwiwa tsakanin a tsaro, da kuma kokarin yaki da ta’addanci.
Ya ce yarjejeniyar ta kuma tabbatar da ‘yancin kare kai kamar yadda aka bayyana a karkashin Mataki na 51 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
“Yarjejeniyar ba ta shafi kowace kasa ba kuma a bude take ga dukkan kasashen ‘yan’uwa da ke neman zaman lafiya, wadata da kwanciyar hankali a yankinmu,” in ji Erdogan.
Ya kara da cewa Türkiye, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufarta ta goyon bayan warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya, bisa girmama dokokin kasa da kasa da kuma bisa hangen nesanta na mallakar yanki.
Erdogan ya ce ya yi tafiya zuwa Makka a ranar Juma’a bisa gayyatar Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, inda ya gana da yariman da Fira Ministan Pakistan Shehbaz Sharif.
Saudiyya, Pakistan da Turkiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a Makka a ranar Juma’a, wadda aka kira ta da “Yarjejeniyar Tsaron Juna.”
A cewar wata sanarwa ta hadin gwiwa da kasashen uku suka fitar, yarjejeniyar ta “kariya ce da hadin gwiwa,” ma’ana duk wani hari da makami da aka kai wa daya daga cikin membobin uku za a dauke shi a matsayin hari kan dukkan ukun.