Iran Da Oman Suna Gab Da Kulla Yarjejeniya Kan Hurmuz

yarjejeniya kan hurmuz da ake gab da cimmawa tsakanin oman da iran zara kai ga bude mashigar hurmu ne bayan an yadda amurka take aiki

Minsitan harokokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa Iran da Oman suna gab da cimma matsaya kan yarjejeniyar yadda za’a kula da mashigar Hurmuz, sai dai bude mashigar ruwan mai muhimanci ya dogara ne da inda kasar Amurka ta yi aiki da yarjejeniyar islam Abad da ake cimma tsakanin su tun a kwanakin baya.

Tattaunawa da kasar Oman kan muhimman batutuwan da suka shafi yadda zaa tafiyar da mashigar Hurmuz, da suka hada da fitar da hanyoyi da jirage za su fi ta ruwan , yanzu haka ana gab da kulla yarjejeniya akai, sai dai bude mashigar baki daya ya doru ne kan wasu sharudda da suka hada da biyan diyya na keta yarjejeiyar Islamabad da aka kulla tsakaninta da kasar Amurka

Babban jami’in diplomasiyar ya bayyana cewa an gudanar da tataunawa tsakanin kasashen biyu bangaren soji da kuma sojin ruwa bisa taswirar ruwa da ake da ita, ana kammalawa za’a tantance sabuwar hanyar da zaa yi amfani da ita

Minstan yace iran ta riga ta yi aiki da kuduri na 5 a yarjejenyar Islamabad da aka cimma wanda zai sanya tsarin zirga-zirgar surfurin ruwa zai dawo yadda yake acikin wata guda, ya kara da cewa Washington ta yi kokarin samar da wata hanyar ta daban a mashigar Hurmuz da niyyar yin watsi da sabon tsarin da iran ta fitar duk da gargadi da Tehran ta yi mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted