Jamhuriyar Musulinci Ta Iran, ta gindaya sharidda guda shida domin sake bude mashigar ruwa ta Hormur.
Da yake sanar da hakan Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Mohammad Baqer Zolqadr ya zayyano sharudda guda shida don sake bude Mashigin Hormuz, yana mai cewa hanyar ruwan za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai Amurka ta canza halayenta ga Iran.
A cikin wani sako, Jami’in na Iran ya bayyana abin da zai zama gyara ga halayen Amurka.
Ya ce ya kamata Amurka ta bi wadannan sharudda guda shida:
1. Amurka ta dakatar da barazana ga Iran ko kuma ta zagi al’ummar wannan kasa.
2 Ta kawo karshen yaki da zaluncin da ake yi wa Iran da kawayenta na Iran a Lebanon, Palestine, Yemen da Iraki har abada.
3 Ta dage shingen da ta yi wa tashihin jiragen ruwa ta kuma janye sojojinta (na ruwa da na sama) daga kewayen Iran.
4 Ta biya diyya ga Iran sakamakon yake-yake zalunci.
5 Ta dage haramtaccen takunkumin marar adalci ga al’ummar Iran.
6 Ta saki kadarorin da aka toshe da kuma waÉ—anda aka sace na al’ummar Iran ba tare da wani sharadi ba.”
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Zolqadr ya bayyana cewa wadannan bukatun al’ummar Iran ne, da suka bayyana su ta hanyar kasancewa “a fagen daga da kuma a kan tituna” na tsawon kwanaki 160.