Search
Close this search box.

Isra’ila Ta Kasha Karin Falasdinawa 25 Da Jikkata Wasu 81 A Cikin Awanni 24 Da Suka Gabata

Isra’ila na ci gaba da zazafa kai hare-hare a sassan zirin Gaza. Na baya baya nan su ne sabbin hare hare da Isra’ila ta kaddamar

Isra’ila na ci gaba da zazafa kai hare-hare a sassan zirin Gaza.

Na baya baya nan su ne sabbin hare hare da Isra’ila ta kaddamar a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa daruruwan Falasdinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin kaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.

Ganau sun ce an kai hare-hare da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka kashe mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, a cewar wata majiyar lafiya da kuma kungiyar Red Crescent ta Falasdinawa.

Ma’aikatar Lafiya a Gaza, ta ce Falasdinawa 25 ne aka kashe sannan 81 suka jikkata a cikin awanni 24 da suka gabata.

Kawo yanzu Alkalumman Falasdinawan Da Isra’ila ta kashe ya kai 37,925 yayin da 87,141 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya ta yankin.

A wani labarin kuma Sojojin Isra’ila sun yi kiyasin cewa ana bukatar karin makwanni hudu don kammala aikin soji a yankin Rafah da ke kudancin Gaza.

Wani rahoto da gidan talabijin na Channel 12 na Isra’ila ya fitar ya ce sojoji na bukatar karin makonni da dama domin kawar da ragowar hanyoyin kasa da ke cikin birnin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments