Iran : ‘Yan Takaran Zaben Shugaban Kasa Na Muhawara Ta Biyu A Gidan Talabijin

‘Yan takara biyu da ke neman kujerar shugabancin kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun fara tafka muhawara ta biyu da ake watsawa kai tsaye a gidan talabijin din kasar gabanin zaben da za;a gudanar a ranar Juma’a. Wannan dai shi ne karo na biyu cikin muhawara guda biyu gabanin zaben na ranar 5 […]
Isra’ila Ta Kasha Karin Falasdinawa 25 Da Jikkata Wasu 81 A Cikin Awanni 24 Da Suka Gabata

Isra’ila na ci gaba da zazafa kai hare-hare a sassan zirin Gaza. Na baya baya nan su ne sabbin hare hare da Isra’ila ta kaddamar a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa daruruwan Falasdinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin kaurace wasu yankuna masu yawan jama’a. Ganau sun ce an kai hare-hare […]
UNRWA Ta Yi Allah-wadai Da Dokar Tilastawa Falasdinawa Yin Hijira Daga Khan Younis

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi Allah-wadai da sabon umurnin Isra’ila na kwashe kimanin mutane 250,000 daga Khan Younis a daidai lokacin da babu kusan wani yanki mai aminci a fadin Gaza”. “Makonni kacal bayan da aka tilasta wa mutane komawa Khan Younis da ya lalace, hukumomin Isra’ila […]
MDD : Ana Bukatar Samun Cikakkiyar Tsagaita Wuta Domin Agaji Ya Samu Kwarara Zuwa Gaza

MDD, ta bayyana cewa ana bukatar samar da cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin domin samuwar kwararar kayan agajiu zuwa Gaza. Domin agaji ya kwarara zuwa Gaza, akwai bukatar a samar da ‘cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin’ Kamar yadda, Sigrid Kaag, jami’ar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, ta bayyana wa […]
Yemen : ‘Yan Houthi Sun Kai Hari Kan Jiragen Ruwan Isra’ila, Amurka, Da Burtaniya A Teku

Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen ta sanar cewa ta kaddamar da sabbin hare haren soji kan jiragen ruwa a Bahar Maliya, da tekun Arabian da Bahar Rum da Tekun Indian Ocean, a matsayin ci gaba da nuna goyan baya ga Falasdinawa a Gaza dake fuskantar hare haren […]
Rasha Ta Gargadi Kasashen Dake Shirin Bai Wa Ukraine Makamai

Kasar Rasha ta sake gargadin kasashen dake kokarin bai wa Ukarine makamai. Rasha ta yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da ta karbi shugabancin kwamitin tsaro na MDD na wannan watan Yuli. Vassily Nebenzya, wakilin Rasha a MDD, ya bayyana gataron taron ‘yan jarida cewa : duk wani mataki na bai wa Ukraine makamai […]
Iran Ta Ce: Barazanar ‘Yan Sahayoniyya Na Kai Hari Kan Lebanon Dabi’ar Dabbobi Ne

Makaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Barazanar da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Lebanon lamari da ke bayyana irin dabi’arsu ta dabbanci Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri a tattaunawarsa ta hanyar wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan kan batutuwan da suka shafi alakar kasashen […]
Rundunar Sojin H.K.Isra’ila Ta Ce: Sojojin Sahayoniyya 668 Suka Halaka A Yakin Gaza

Rundunar sojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa: Sojojin yahudawan sahayoniyya 668 suka halaka tun bayan kaddamar da yaki kan Zirin Gaza naFalasdinu Alkaluman da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka fitar na nuni da cewa: Adadin sojojin yahudawan sahayoniyya da aka kashe tun farkon fara kai hare-haren wuce gona da iri […]
Fiye Da Hafsoshin Sojin Yahudawa 800 Ne Suka Mika Takardar Yin Murabus Daga Ayyuykansu

Sama da hafsoshi sojin haramtacciyar kasar Isra’ila 800 ne suka mika takardar yin murabus daga ayyukansu a wannan shekara Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun watsa labari a jiya, Litinin cewa: Fiye da jami’ai sojin yahudawan sahayoniyya 800 ne masu matsayi na Kanar da Laftanar Kanal suka mika takardar yin murabus dinsu daga aiki […]
Shugaban Kasar Mauritaniya Ya Sake Samun Nasarar Zaben Shugabancin Kasar Karo Na Biyu

Shugaban kasar Mauritaniya ya samu gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa karo na biyu a kasar Mauritaniya Hukumar zabe a Mauritaniya ta sanar da nasarar shugaba Mohamed Wuld Ghazouani mai barin gado a wa’adi na biyu na shugabancin kasar bayan samun kuri’u sama da kashi 65 cikin dari na kuri’un masu zabe, yayin da dan […]
Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Ya Sanar Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da kafa gwamnatin hadin kan kasa da ta kunshi ‘yan adawa tare da jam’iyyarsa ta National Congress Party. Ramaphosa ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar tahanyar kafar talabijin din kasar a yammacin ranar Lahadi, inda ya bai wa jam’iyyun adawa a sabuwar […]
Iran: ‘Yan Takarar Zaben Shugaban kasa Zagaye Na Biyu Sun Tafka Muhawara Ta Farko

‘Yan takara biyu da ke neman shugabancin kasar Iran da za su kara a zabe zagaye na biyu Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun tafka muhawarar farko ta talabijin, domin gabatar da shirye-shiryensu kan batutuwan siyasa da tatatlin arziki da inganta rayuwar jama’a da ci gaban kasa. Wannan shi ne karo na farko daga cikin […]
Alkaluman EU: Turkiyya ta dawo da shigo da mai daga Iran a watan Maris

Alkaluman da hukumar kididdiga ta Tarayyar Turai Eurostat ta fitar na nuna cewa, a watan Maris din bana ne Turkiyya ta dawo da shigo da mai daga Iran kusan shekaru hudu bayan da ta yanke jigilar kayayyaki zuwa sifiri don yin aiki da takunkumin Amurka kan Tehran. Bayanai na Eurostat da kamfanin dillancin labaran IRNA […]
Kungiyar kasashen Larabawa ta cire Hizbullah daga cikin wadanda take kira kungiyoyin ta’addanci

Kungiyar hadin kan Larabawa ta janye daga matsayinta na sanya kungiyar Hizbullah a matsayin “kungiyar ta’addanci”, Hossam Zaki, mataimakin sakatare-janar na kungiyar Larabawa ya sanar da hakan. Zaki ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka watsa ta tashar talabijin ta Al-Qahera ta Masar cewa, “A cikin hukunce-hukuncen kasashen Larabawa da suka gabata, an sanya […]
Salmiya: Sojojin Isra’ila Sun Azabtar Da Ni

Daraktan asibitin al-Shifa na Gaza, wanda sojojin Isra’ila suka tsare da shi sama da watanni bakwai, ya ce an gallaza masa azaba mai tsanani a lokacin da ake tsare da shi a gidajen yarin Isra’ila. Mohammed Abu Salmiya na daga cikin Falasdinawa sama da 50 da Isra’ila ta sako da suka koma Gaza, a cewar […]
Dakarun Yemen sun kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila, Amurka da Birtaniya

Dakarun Yaman sun sanar da kaddamar da hare-hare guda hudu kan jiragen ruwa na gwamnatin Isra’ila, da Amurka da Birtaniya, wadanda dakarun na Yemen suka yi wa farmakin lakabi da “Trio of Evil.” Kakakin rundunar sojin gwamnatin san’a Birgediya Janar Yahya Saree ne ya sanar da ayyukan farmakin a cikin wata sanarwa da ya fitar. […]