Isra’ila ta kai hare-hare a Dahiyeh babban birnin Lebanon

Gwamnatin Isra’ila ta kai hare-hare a yankunan kudancin Beirut, babban birnin Lebanon duk da kin amincewar Amurka da cewa irin wadannan hare-hare na iya haifar

Gwamnatin Isra’ila ta kai hare-hare a yankunan kudancin Beirut, babban birnin Lebanon duk da kin amincewar Amurka da cewa irin wadannan hare-hare na iya haifar cikas ga yunkurin cimma yarjejeniyar dakatar da yaki a yankin.  

Rahotanni sun ce an ji karar fashewar abubuwa da dama a Dahiyeh da ke Beirut inda hedikwatar Hezbollah ta ke.

Sun ce harin ya nufi wani gini da ke yankin Al-Mreijeh da makamai masu linzami guda uku.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan yakin gwamnatin Isra’ila, Israel Katz, sun fada a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan hedikwatar Hezbollah.

Sun yi ikirarin cewa harin ya mayar da martani ne ga ci gaba da harba makamai masu linzami zuwa yankunan arewacin Isra’ila da ta mamaye.

A farkon wannan watan Isra’ila ta dakatar da shirin kai hare-hare kan Dahiyeh bayan da aka ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa Netanyahu a cikin kiran gaggawa na wayar tarho cewa kai hari a Beirut abu ne da Washington ba zata aminta da shi ba.

Hare-haren da Isra’ila ta kai a Lebanon kwanan nan sun kashe dubban mutane tare da korar kusan mutane miliyan biyu a kasar Larabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted