Isra’ila Na ci Gaba Da Zubar Da Jinin A Kasar Labanon Duk Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu guda 25 kuma suka jikkata a ci gaba da hare haren

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu guda 25 kuma suka jikkata a ci gaba da hare haren da isra’ila ke kai wa a gabashin kasar Labanon, inda hare haren suka fi Kamari a yankunan bikaa da suka hada da riyaq, bednayel, Asarnab kamar yadda gidan talabijin na Al’mayadden ya bayyana.

haka zalika ko a jiya jumaa ma Isra’ila ta kai hare-hare a sansanin yan gudun hijira na Ain al-hilweh dake kudancin garin saida kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 2 tare da jikkara wani adadi mai yawa.

wadannan hare-haren suna zuwa ne a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin kungiyar hizbullah da isra’ila  tun a ranar 27 ga watan nuwamba na shekara ta 2024, inda kudurin majalisar dinkin duniya mai lamba 1701 na shekara ta 2006 ya bukaci a mutunta hurumin kasar labanon

 A kudancin labanon ma jiragen yaki HKI sun kai wasu hare-hare a yankin shara dake kusa da Titin Nabi dake yankin bikaa sai dai babu wani karin bayani game da irin asarar da hakan ya haifar,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted